Majalisa ta amince da kasafin kudin Bauchi

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Kasafin kudin bana a jihar Bauchi ya kai naira biliyan dari da talatin da biyar

A Najeriya, yayin da jama'a ke ci gaba da kokawa da matsanancin halin rayuwa, wani batu da ke daukar hankalin al'umma shi ne na kasafin kudi a matakan gwamnati daban-daban, inda a makon jiya Majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudi na gwamnatin tarayya na kimanin Naira tiriliyan shida, wanda shi ne mafi girma a tarihin kasar.

Ana dai zargin gwamnatoci da kasa aiwatar da kasafin kudi yadda yakamata domin jin dadin jama'a a Najeriya.

Shi ma Gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, a karshen makon da ya gabata ya sa hannu kan kasafin kudin jihar kimanin naira biliyan 135, wanda Majalisar dokoki ta amince da shi ya zama doka.

Gwamnan ya kuma tabbatarwa da al'ummar jihar cewa za a aiwatar da kasafin kudin sau da kafa, domin amfaninsu.