Jirgin sojoji ya fado a Algeria

Image caption Jirgin mai saukna ungulu ya fado a yankin Tamanrasset da ke kudancin Algeria, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 12.

Ma'aikatar tsaron Algeria ta ce wani jirgi mai saukar ungulu na sojoji ya yi hadari a kudancin kasar, inda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 12.

Jirgin, kirar kasar Rasha, MI-171, ya fado ne a yayin da yake gudanar da wani aiki a yankin Tamanrasset, wanda ke da nisan kilomita 2,000 daga Algiers, babban birnin kasar.

Ma'aikatar ta ce alamu sun nuna cewa, jirgin ya samu matsala ne ta na'ura, amma ba a tabbatar da musabbabin dalilin ba tukunna.

Masu sukar lamiri sun ce ko a da can, kasar ta Algeria bata kula da lafiyar jiragenta.

A shekarar 2014 mutane 77 sun hallaka sakamakon faduwar wani jirgi, kazalika a shekarar 2012 ma wasu jiragen sojoji biyu sun yi karo yayin gudanar da wani aikin horo, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matuka jirgin su biyu.

Ba a tabbatar da ko wane aiki jirgin ya je aiwatarwa ba.

A shekarar 2014 ma kasar Vietnam ta tsayar da jiragen ungulunta kirar MI-171 baki daya, bayan da wani hadari da ya afku a garin Hanoi ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 18.