An murkushe mayakan Al-shabab

Hakkin mallakar hoto AP

Mahukunta a jihar Galmudug dake Somalia, sun ce sun murkushe mayakan al-Shabab da suka tsere daga yankin arewacin kasar.

Mahukuntan sun ce an kashe 'yan kungiyar Al-Shabab sama da dari, an kuma kama wasu gwammai a kwanaki 4 da aka kwashe ana gumurzu.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da adadin mutanen.

Wannan dai ya biyo bayan fadan da aka kwashe kwanaki ana yi tsakanin kungiyar al-Shaab da dakarun soji daga yankin Puntland, mai dan kwarya kwaryar cin gashin kai dake iyaka da jahar Galmudug.

Masu fafutukar Islamar sun tsere zuwa arewaci, bayan da aka fatattake su daga kudanci da tsakiyar Somalia.