Angola: 'Yan tawaye zasu sha dauri

Image caption Masu zanga-zangar sun yi kira da shugaba Jose Eduardo dos Santos, da ya yi murabus, bayan ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar.

An yake wa wasu masu fafutuka na kasar Angola su 17 hukuncin zaman kaso tsakanin shekaru 2 zuwa 8 bisa shirya yin tawaye kan shugaba Jose Eduardo dos Santos.

Daya daga cikinsu wani shaharraren mawaki ne mai suna Luaty Beirao, da aka fi sani da Ikonok-lasta, wanda a bara ya yi yajin cin abinci na wata guda.

An kama matasan ne bayan da suka tattauna kan wani littafi game da turjiya cikin lumana.

Har wa yau kungiyarsu ta gudanar da zanga-zanga tana neman Mr Santos, wanda ke mulkin Angola na tsawon shekaru 36, da ya yi murabus.