'Tukwicin miliyan 1 kan bayanin sace Kanal'

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Rundunar soji ta sha alwashin ba da tukwici kan bayanin sace Kanal

<span >Hukumomin rundunar sojin Najeriya sun sha alwashin tukwicin naira miliyan daya ga duk wanda ya bayar da bayani mai amfani da zai sa a gano yadda za a kubutar da jami'insu da aka sace, Kanal Sama'ila Inusa.

Rundunar sojin ta ce za ta bayar da cikakkiyar kariya ga duk wanda ya samar da bayani, kuma za a boye sunansa.

An sace Kanal Inusa ne a motarsa kirar Mercedes-Benz a kusa da Kamazo kan titin hanyar zuwa matatar man fetur da ke karkashin karamar hukumar Chikun.

Wata sanarwa da mai magana da yawun runduna ta daya Kanal Abdul Usman ya fitar, ta ce "mutanen da suka sace Kanal din sun sauke matarsa ne sai suka wuce da shi tare da motar tasa.