Boko Haram sun sace min yara na a Chadi

Image caption Djibrilla ya rasa yara biyar, duk da cewar daya ya dawo gida.

An yi nasarar cin karfi da kuma korar yawancin 'yan kungiyar Boko Haram daga cibiyar su da ke arewacin Najeriya a shekarar da ta gabata, inda hakan ta sa suka kaurace zuwa kasar Chadi da ke makwabtaka.

Wakilin BBC Thomas Fessy, ya gana da wani iyali da ayyukan kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulinci ta daidaita.

Djibrilla, magidanci ne mai shekaru 64, ya zauna shiru a lungu, cikin bukkarsa da iskar da ke tattare da kura ke shiga.

Watanni da dama sun wuce, tunda aka sace biyar daga cikin yaransa takwas, wadanda basu fi shekarun tsakanin biyu da 15 ba.

Shin ina suke? Wani hali suke ciki? An tilasta masu shiga yaki ne? Tambayoyi da dama da bai iya bayar da amsarsu.

"Har yanzu ban fahimci lamarin ba, duk kokarin da nake yi." In ji Djibrilla.

"Na yi matukar kaduwa, saboda basu kai shekarun da za su iya kare kansu ba." Ya kara da cewa, "Na bar wa Allah komai, saboda babu abun da zan iya yi."

An sace yaran ne su biyar, bayan wani hari da aka kai a kauyen su.

Wadanda suka sha da kyar, kamar Djibrilla ne yanzu ke zama a wani sansani dake kauyen, wanda ire-iren su ke tasowa tsakankanin rairen hamada a tafkin chadi, da ke tsakanin kasashen Najeriya da Chadi.

Image caption Yawanci mutane da ke yankin sun dogara ne da kamun kifi.

Hare-Haren Boko Haram ne ya tilastawa 'yan gudun hijiran da suka taso daga wasu tsibirai zaman hamada, inda basu iya ci gaba da sana'arsu ta kamun kifi, da noma.

Kazalika sojojin Chadi ma sun basu shawarar barin gidajen su, domin kar 'yan ta'addan su sake tunkarar su.

Image caption 'Yan kauyen yanzu na zama ne cikin hamada.

Kasashen Chadi da Najeriya da Kamaru da Nijar na cikin kasashen da suka hada gwiwar rundunar sojojinsu, domin ganin sun yaki kungiyoyin ta'addan, wadanda suka kai wa duk kasashen nasu.

Ga alamu dai babu wani dauki da kauyen da Djibirlla ke zaune ke samu.

Yana zaune cikin bakin ciki dai, sai a samu rana cike da farin ciki, kamar yadda ya bayyana, inda kawai a watan Satumba, sai sojoji suka dawo masa da babban dansa.

'Alkawarin makuden kudade'
Image caption Wasu matasa biyu sun ce an ja ra'ayinsu ne da alkawarin cewa zasu samu kudade masu yawa.

Youssouf, (ba asalin sunansa ba), yana da shekaru 26, kuma ya baro gida tun kafin a sace sauran 'yan uwansa.

Ya shiga cikin kungiyar 'yan ta'addan da kansa ne, kuma ba shi kadai ya yi hakan ba.

"Wasu maza ne suka zo kauyen mu, suka ce mu zo mu shiga kungiyar Boko Haram" In ji Adam(shi ma an sakaya sunan sa).

Yana shekaru 16 ya shiga kungiyar, kuma ya kwashe watanni biyu tare da kungiyar a shekarar da ta gabata.

Youssouf da ke gefensa, shi ma ya ce, "Toh mun zaune ba aikin yi, kuma sun ce mana zamu samu kudi masu yawa."

Ya kara da cewa, "Sun ce zamu samu duk abunda muke bukata na rayuwa."

Yawanci matasa a yankin basu da cikakken ilimin boko, sai abun da suke samu a marantar allo.

Image caption Har yanzu mayakan Boko Haram na ci gaba da fiddo bidiyo domin kara wa mayakansu kwarin gwiwa.

Kazalika babu ababan more rayuwa a yankin, ga matsanancin talauci da mutanen garin ke fama da shi.

Hakan kuma ta haddasa fadawar matasan a hannun Boko Haram, wadanda suka kwadaita masu da jan ra'ayi ga rayuwa mafi inganci da wadata.

Hadakar sojojin kasashen dai sun ci karfin kungiyar ta Boko Haram, duk da cewar har yanzu tana barazana ga tafkin chadi.

"Babu wani kudi da muka samu" In ji Youssouf.

Sojojin Chadi sun tsare shi na wata daya, a barikin su, daga bisani suka maido shi wajen mahaifinsa.

"Na yi matukar farin ciki da yarona ya dawo" In ji Djibrilla, "amma na yi masa gargadi, dole ka zauna da mu koda muna cikin matsanancin talauci ne".

Duk da haka dai Djibrilla na begen sauran 'ya'yansa da har yanzu babu labarin su.