'Karkatar da jirgin Masar ba ta'addanci ba ne'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sace wani jirgin sama na Fasinjoji a Masar

Shugaban kasar Cyprus, Nicos Anastasiades ya ce mutumin da ya karkatar da jirgin saman da ya taso daga birnin Iskadariyya zuwa birnin Alkahira na kasar Masar, zuwa Cyprus, ba dan ta'adda ba ne.

Rahotanni dai sun ce mutumin ya aikata hakan ne domin kwadayin haduwa da matarsa 'yar kasar Cyprus wadda take kan hanyarta ta zuwa filin jirgin.

Direban jirgin ya ce mutumin ya tilasta masa karkatar da akalar jirgin ne bayan da ya fada musu cewa yana dauke da bama-bamai.

Jirgin dai yana dauke da fasinjoji fiye da 80 kuma yanzu haka mafi yawancinsu sun sauka.