Sarkin Kano ya shawarci 'yan kasuwa

Image caption Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shawarci 'yan kasuwa da su rinka kai kudaden su ajiya bankuna

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya shawarci 'yan kasuwa da su rinka kai kudadensu ajiya bankuna maimakon barin su a shaguna, a wani mataki na rage yawan asara a lokacin gobara.

Sarkin wanda ya katse ziyarar da yake a kasahen waje inda ya koma gida, ya yi kira ga hukumomi a matakin jiha da gwamnatin tarayya da su tsananta bincike domin gano musabbanin abinda ke janyo afkuwar gobara musamman a kasuwanni.

Rahotanni sun ce sama da shaguna 5,000 ne suka kone, inda kuma aka kiyasta cewa an rasa dukiya ta biliyoyin Nairori.

A halin da ake ciki Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti domin bayar da shawara ta gaggawa kan abinda ya kamata gwamnati ta yi wa 'yan kasuwar da bala'in gobarar ya afka musu.

Ga dai abinda Mai martaba sarkin ke cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti