Mutane 1,000 sun tsere daga Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akasarin su mata ne da kananan yara kuma sun ce jama'a na ci gaba da ketara wa zuwa yankin Noumbiel.

Jami'ai a kasar Burkina Faso sun ce fiye da mutane duba daya ne suka ketara kan iyakar kasar zuwa Ivory Coast.

Akasarin su dai mata ne da kananan yara kuma sun ce jama'a na ci gaba da ketara wa zuwa yankin Noumbiel inda suke fama da rashin kulawa.

Fiye da mutane dari biyu kuma sun ketara zuwa kasar Ghana, kuma galibin su suna tsere wa rikici ne da ake yi tsakanin makiyaya da manoma kusa da garin Bouna da ke arewa maso gabashin kasar.

Akalla mutane goma sha bakwai ne aka kashe yayin da wasu da dama suka samu raunuka a rikicin.