Kamfanin NTT Data na sayen kayayyaki daga kamfanin Dell

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfanin kasar Japan na NTT Data na sayan kayan fasahar kere-kere daga Kamfanin Dell

Kamfanin kasar Japan na NTT Data na sayan kayan fasahar kere-kere daga Kamfanin Dell na fiye da dalan Amurka biliyan 3, kwatankwacin Fan biliyan 2.1.

Hakan ya zo ne saboda yunkurin fadada harkokinsa da yake yi izuwa Arewacin Amurka.

Wannan ne kusan harka mafi girma da kamfanin NTT Data ya taba yi a matsayin kamfani mafi dadewa da ya mallaki harkokokin sadarwa a kasar Japan.

An samu labarin cewa, kamfanin Dell na neman sayar da wasu hannayen jarinsa na harkokin da ba muhimmai bane domin ya samu shigar miliyoyin daloli a kan kudaden da ya kai dala biliyan 67, bisa ga mallakar ma'ajiyin bayanai na kamfanin EMC Corp da ya yi.

Kamfanin NTT Data zai dauki ma'aikata dubu 28 a Arewacin Amurka da kuma Indiya.

Bloomberg Data ya ce NTT Data ya kashe fiye da Yen biliyan 72 wajen sayan kamfanonin kasashen waje tun shekara ta 2011.

Abokanan huldarsa sune India's Tata Consultancy Services da France Atos da kuma kamfanin Cognizant Technology Solutions na kasar Amurka.