Gobarar Kano ta shafe mu - Niger

Image caption Kungiyar 'yan kasuwar Nijar ta jajantawa takwarorinta na kasuwar sabon gari

Kungiyar 'yan kasuwa a Jamhuriyar Nijar ta bayyana alhinin ta dangane da mummunar gobarar da ta tashi, a babbar kasuwar sabon gari da ke Kano.

Rahotanni sun ce sama da shaguna 5,000 ne suka kone, inda kuma aka kiyasta cewa an rasa dukiya ta biliyoyin kudi.

Ga dai karin bayanin da shugaban kungiyar 'yan kasuwar ta Nijar, Alhaji Sama'ila Mai Aya, ya yi wa wakilinmu BARO ARZIKA a Yamai.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti