Gwamnati za ta fara jin ra'ayoyin 'yan kasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnati na son jin ra'ayoyin 'yan kasa kan wasu al'amura

<span >Gwamnatin Nigeria ta ce za ta fara wani taro na jin ra'ayoyin 'yan kasar.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Abuja.

A cewarsa, gwamnati ta yanke shawarar yin irin wadannan taruka ne saboda ta fahimci amfanin yada labari da sadarwa a wajen al'umma musamman ma na karkara.

Ya ce, "Tuni akwai shirin da aka fara wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai fara irin wadannan taruka a yankunan kasar."

Garba Shehu ya kara da cewa, "Don haka za a yi ne jiha-jiha. Gwamnati ta gano amfanin bukatar kai wa mutane bayanai, don haka an dauki matakai domin yin hakan."

Ana ganin wannan taro na jin ra'ayin 'yan kasa a matsayin wanda zai basu damar fayyace ra'ayinsu da kuma bai wa gwamnati shawarar kan yadda za a ciyar da kasar gaba.