Pakistan: Ana kame kan harin Lahore

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama na cikin alhinin harin
Rundunar sojin Pakistan ta ce an kama mutane da yawa a sassa daban-daban na kasar, kwana daya bayan da wani bam ya kashe mutane fiye da 70 a Lahore.

Kakakin sojin kasar ya ce, an kuma kama wani babban tarin makamai.

Bam din ya tashi ne a wani dandalin da iyalai da yawa suka hallara a ranar Lahadin da ta gabata domin bikin Easter.

Wani bangare na kungiyar Taliban a Pakistan -- Jama'atul -Ahrar -- ya ce da gangan ya hari Kiristocin Lahore 'yan tsiraru.

Ana dai jana'izar da dama daga cikin wadanda abun ya shafa.

Firai Ministan Pakistan Nawaz Sharif, ya ce, zai kawar da 'yan ta'addan da suka kashe 'yan kasarsa maza da mata.

Karin bayani