Amurka: An killace fadar White House

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun yi musayar wuta da wani ahrbi a Majalisar Dokokin kasar Amurka, inda daga bisani aka kama shi, duk da cewar wani dan sanda ya raunata.

Rahotannin da aka samu daga Washinton na cewa an kama dan bindigan, duk da cewar an harbetare da jikata wani jami'in dan sanda amma bai yi tsanani ba.

Rahotanni sun ce an yi harbe-harbe a wata cibiyar saukar baki a Majalisar Dokokin Amurka, wanda aka sani da US Capitol.

Shaidu sun ce an umurce su da neman mafaka ta hanyar amfani da na'urar fadada murya.

An umurci 'yan jaridu da ke wani yankin da aka kebewa manema labarai a US Capitol din da su tsaya wuri guda.

Haka nan ma an rufe fadar shugaban kasar ta White House.

Wata kakakin 'yan sandan majalisar ta ce bata da cikakken bayani a yanzu, amma nan bada jimawa ba za su fitar da sanarwa.