Buhari ya ki sanya hannu kan kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun a karshen shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2016 ga majalisa

<span >Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu kan kasafin kudin bana har sai an tura masa cikakkun bayanan kasafin kudin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani babban jami'in gwamnati na cewa, majalisar dokokin kasar wadda ta zartar da kasafin a makon da ya gabata ta aike masa da kasafin kudin amma ba wani cikakken bayani.

An gabatar da kasafin kudin na kimanin dala biliyan 30 wanda ba a taba kasafi mai yawa irinsa ba, don farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya tabarbare sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya.

A farkon shekarar ne shugaba Buhari ya kori jami'ai da dama da ake zargi da aringizon kasafin kudin inda suka kara miliyoyin nairori domin batarwa a wasu hukumomin gwamnati.