Matsayin Buhari a taron nukiliya a Amurka

Image caption Shugaba Buhari zai gana da shugaba Obama na Amurka.

A ranar Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ta shi zuwa birnin Washington na Amurka don halartar babban taro a kan nukiliya da kuma tsaro da za'a fara ranar Alhamis.

Ana saran shugaba Buhari zai hadu da shugaba Barack Obama da sauran wasu shugabannin kasashen duniya 60 da ke halartar taron.

Taron dai zai tattauna a kan takaita yaduwar makaman nukiliya, inda ake saran shugaba Buhari zai jaddada matsayin Najeriya na goyon bayan kasashen duniya a kan amfani da nukiliya don samar da makamashi da kuma ci gaba.

Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Najeriyar ta ce, a yayin ziyarar, shugaba Buhari da wa su gwamnoni da ke rufa masa baya za su tattauna batutuwa daban-daban da manyan jami'an gwamnatin Amurka da kuma sauran shugabannin kasashen da ke halartar taron.