Ana kokarin ceto matasan arewa a Lagos

Wasu shugabannin al'ummar arewacin Nigeria sun fara wani yunkuri na ceto wasu matasa 'yan arewa sama da 306 da jami'an 'yan sanda da gwamnatin jihar Lagos ke tuhumarsu a gaban shari'a.

Ana zargin matasan da hannu wajen tayar da rikici a kasuwar mile 12, wani rikici da ya haifar da salwantar rayuka da kuma asarar dukiya ta miliyoyin nairori.

Dan majalisar wakilai na tarayya, Honorabul Mohammad Sani Zoro, ya nuna bukatar gwamnonin arewa su saka baki domin shiga tsakani don a sassauta sharuddan da aka gindaya wajen bayar da beli ga matasan, da kuma duba yiwuwar sako su.

Ga dai yadda hirarsu ta kasance da wakilinmu Umar Shehu Elleman:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A farkon watan Maris ne rikici ya barke a Mile 12 tsakanin 'Area Boys' wadanda galibinsu Yarbawa ne, da kuma 'yan acaba wadanda galibinsu Hausawa ne 'yan arewacin kasar.

Karin bayani