An kama wanda ya karkatar da jirgin Masar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'an tsaro sun kama mutumin da ya karkatar da jirgin.
Ma'aikatar harkokin wajen Cyprus ta ce an kama mutumin da ya karkatar da jirgin saman da ya taso daga birnin Iskandariyya zuwa birnin Alkahira na kasar Masar, zuwa Cyprus, bayan da aka kawo karshen lamarin.

Rahotanni dai sun ce mutumin ya aikata hakan ne domin kwadayin haduwa da matarsa 'yar kasar Cyprus wadda take kan hanyarta ta zuwa filin jirgin.

Direban jirgin ya ce mutumin ya tilasta masa karkatar da akalar jirgin ne bayan da ya fada musu cewa yana dauke da bama-bamai.

Jirgin dai yana dauke da fasinjoji fiye da 80 kuma yanzu haka mafi yawancinsu sun sauka.

Karin bayani