Hama Amadou zai dawo daga Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hama Amadou ya sha kaye a zaben da aka gudanar na shugaban kasa a Nijar

<span >Jagoran babbar jam'iyyar adawa na jamhuriyar Nijar Hama Amadou, wanda ke asibiti a Faransa zai koma gida ranar Laraba.

Likitansa Luc Karsenty ne ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP hakan.

Kafin a kai shi asibitin don bashi taimakon gaggawa bisa rashin lafiyar da yake fama da ita a farkon watan nan, Hama Amadou na tsare ne a gidan yarin Nijar inda ake tuhumarsa da safarar jarirai.

Amma ya yi watsi da wannan tuhuma, ya ce salon bata masa suna a siyasance ne kawai.

Rahotanni sun ce tun da fari dai hukuncin kotun na bayar da belin nasa na nufin ba zai koma gidan yarin ba, idan ya koma kasar tasa.

Karin bayani