Faransa ta kwato makamai a tekun Indiya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rundunar sojin ruwan Faransa, ta ce ta kwace makamai masu tarin yawa a wani jirgin kwale-kwale a tekun Indiya.

Makaman sun hada da Machine gun, da makamai masu tayar da tankokin yaki, kuma ana zargin za a kai su kasar Somaliya ne, inda majalisar dinkin duniya ta sanya takunkumin hana kai makamai.

Wakilin BBC ya ce rundunar hadin gwiwar ta ce kaman wata babbar nasara ce, koda yake basu bayyana komai ba kan wadanda suka yi safarar makaman.

A farkon watan nan, sojojin ruwan Australia sun kame wani jirgin kamun kifi dauke da daruruwan makamai. An kuma ce su ma an nufi Somaliya da su ne.