Niger: An bayar da belin Hama Amadou

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon firaiministan Niger, Hama Amadou

Kotun daukaka kara a jamhuriyar Niger, ta ba da belin tsohon kakakin majalisar dokoki kuma dan takarar shugabancin kasar, Hama Amadou wanda yake tsare a gidan yari tun watan Nuwamba.

A ranar 14 ne ga watan Maris ne kotun ta yi wani zama domin duba bukatar da lauyoyin Hama Amadun suka gabatar na neman belinsa.

Ana dai tuhumar Hama Amadou da safarar jarirai daga makwabciyar kasar, Najeriya.

Yanzu haka, Hama yana asibiti a kasar Faransa domin samun kulawa ta musamman.

Hama ne babban abokin hamayyar Mahamadou Issoufou a karawar da suka yi a zagaye na biyu na zaben kasar, a inda kuma Issoufou ya lashe zaben da kaso 92.

Ko a zagaye na farko na zaben, Hama Amadou yana kurkuku aka kada kuri'a.