Nigeria: An ware $13m ga matasa - Dalung

Image caption Ministan matasa da wasanni na Najeriya, Barista Solomon Dalung.

A Najeriya, a wani yunkuri na shawo kan kalubalen da matasa suka dade suna fuskanta, gwamnatin kasar ta ce ta ware kudi naira biliyan 250, kwatankwacin $13m, domin tallafa musu.

Ministan matasa da wasanni na Najeriyar, Barrista Solomon Dalung wanda ya sanar da hakan, ya ce za dai a kasashe kudaden ne domin yin sana'o'i a fannin noma da hakar ma'adinai da kuma ba wa matasan jari.

Barista Dalong ya ce gwamnatin kasar ta dauki matakai na kaucewa kurakuran da ake cin karo da su a baya wajen tallafa wa matasa, wanda a wa su lokutan suke karkatar da kudaden da ake ba su zuwa wasu harkoki na daban.

Barista Dalung ya kuma kara da cewa ma'aikatarsa ta dauki matakai na dawo da martabar kwallon kafa a kasar.

Wasu daga cikin sabbin matakan sun hada da kore yiwuwar daukar kociya daga kasar waje da kuma warware matsalar da ke hukumar kwallon kafar kasar.