BH: Obasanjo ya kai ziyara Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cif Olusegun Obasanjo na daya daga cikin masu daga murya kan batun rikicin Boko Haram.

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya nemi da a sake gina wuraren da rikicin Boko Haram ya lalata.

Rahotanni na cewa Obasanjo wanda yake a birnin Maiduguri na jihar Borno, a wata ziyarar kwana biyu da yake yi a jihar, ya kuma yaba wa gwamnati bisa kokarin da take yi na kokarin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Obasanjo wanda ya je birnin ranar Litinin ya jajantawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa sannan kuma ya je jami'ar Maiduguri da ke birnin, a inda aka yi bikin karrama shi.

Tsohon shugaban kasar ya samu ganawa da Shehun Borno, Garbai El-Kanemi da gwamnan jihar, Alhaji Kashim Shettima.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Obasanjo yake kai ziyara jihar ta Borno, mai fama da rikicin Boko Haram.

A 2011, Cif Obasanjo ya je jihar domin saduwa da sirikin Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Waljihad, da aka fi sani da Boko Haram.