Nigeria: Ministan mai zai bayyana a gaban majalisa

Image caption Dr. Ibe Kachikwu a lokacin da shugaba Buhari yake rantsar da ci

Ministan mai na Najeriya, Ibe Kachikwu zai bayyana a gaban majalisar dattawan kasar domin yi wa zauren bayani kan matsalar karancin man fetur, a kasar.

A ranar Litinin ne majalisar ta dattawa ta aikewa da ministan takardar gayyatar, bayan da 'yan majalisar karkashin jagorancin shugaban kwamitin harkokin man fetur, Sanata Barau Jibril suka zagaya Abuja, babban birnin kasar domin ganin yadda matsalar man take a birnin.

Shugaba Buhari ne dai babban ministan man kasar, a inda shi kuma Ibe Kachikwu shi ne karamin ministan na man.

Da misalin karfe 2:00 agogon Najeriya da Niger ne na ranar Talata, ake sa ran ministan zai bayyana, a zauren majalisar ta dattawa.

Matsalar karancin mai dai ta kwashe fiye da watanni 10 tana addabar Najeriya kuma har yanzu an kasa shawo bakin zaren.