Afrika Ta Kudu: Zaki ya bazama a gari

Hakkin mallakar hoto ALICE HUFFMAN
Image caption Zakin ya kashe dabbobi 30
Wani zaki mai hadarin gaske ga dan adam ya tsinke kuma yana watangaririya a Afrika ta Kudu.

An ce zakin ya kubuce ne daga wani gandun daji ta hanyar rarrafawa ya kuma bi ta karkashin wani gini wanda aka jona masa wutar lantarki.

Zakin, wanda ake yi wa lakabi da 'Sylvester' ya gudo ne daga wajen hutawa na Karoo a kasar ta Afirka ta kudu, ya kuma yi nisan kilomita 300, a inda ya hallaka sauran dabbobi guda 30.

An samu an cafke shi makonni uku bayan nan, ta hanyar sukarsa da allurar kashe jiki da aka yi masa wadda aka harbo daga wani jirgi mai saukar ungulu.

Sai dai a wannan karo, malaman dabbobi suna fatan sake cafke zakin da wuri saboda yana rataye da wata igiya a wuyansa wadda take nuna inda yake.

Karin bayani