Volkswagen ya janye motoci masu amfani da lantarki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An janye motocin ne saboda matsalar da aka gano cewa za su iya dauke wuta yayin da ake amfani da su.

Kamfanin kera motoci na Volkswagen ya janye dubban motocin sa kirar e-Golf daga kasuwanni a Amurka.

Kamfanin ya ce an dauki wannan mataki ne saboda matsalar da aka gano a motocin da ka iya sa su dauke wuta yayin da ake amfani da su.

Wannan ne dai karo na uku a 'yan makwannin nan da ake janye motoci ma su amfani da lantarki daga kasuwanni.

A farkon wannan watan ne kamfanin Nissan ya ce yana bukatar sake manhajar da ke sarrafa birkin motocin sa masu fuka fukai.

Kwanaki kadan bayan wannan sai kuma kamfanin kera motoci na Renault ya ce yana bukatar sake duba wa tare da sauya wasu na'urori da ke cikin birken motocin sa kirar Zoe.

Wasu masana sun ce kasancewar an yi amfani ne da sabbin fasaha da suke da sarkakiya wajen kera motoci masu amfani da lantarkin, ya sa ba su yi mamakin sanarwar janye motocin daga kasuwanni ba.