CAR: An rantsar da Archange Touadera

Image caption Sabon shugaban jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Faustin-Archange Touadera

Da yammacin ranar Laraba ne zababben shugaban jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Faustin-Archange Touadera, ya sha rantsuwar kama aiki.

Mista Touadera wanda tsohon firaiministan kasar ne kuma farfesa kan fannin lissafi.

Ya dai yi alkawarin samar da zaman lafiya, ba tare da nuna banbanci ba da kuma inganta tattalin arzikin kasar.

A ranar ta Laraba ne kuma kasar Faransa take kwashe sojojinta daga jamhuriyar ta Afirka ta yamma, bayan kwashe shekaru kusan uku suna aikin wanzar da zaman lafiya, a kasar.

Tundai lokacin da 'yan tawaye suka tumbuke shugaban kasar Francoise Bozize, a 2013, jamhuriyar ta Afirka ta kudu take fama da rikicin kabilanci da na addini, al'amarin da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da jikkata dubbai.