Fulatanci na fuskantar barazanar gushewa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana iya samun Fulani a kowace kasa ta Afirka kuma suna auren mutanen da ba kabilarsu ba.

Masana sun ce yaren Fulatanci ko kuma Fulfulde yana fuskantar barazana daga wasu manyan yare kamar Turanci da Hausa.

Akwai masu magana da yaren Fulatanci a kasashe masu yawa musamman a Afirka ta yamma kamar Guinea Conakry da Guinea Bissau da Senegal da Mali da Niger da Najeriya.

Sauran su ne Sierra Leone da Burkina Faso da sauran kasashen da Fulani suka warwatsu.

Sai dai kuma masana na ganin cewa manyan yaruka da ke da tasiri a kasashen da Fulanin suke, na yin barazana ga dorewar yaren.

Hakan ne ma yasa jami'ar Bayero ta Kano a arewacin Nigeria ta gudanar da wani taro da nufin bunkasa fulatanci da kuma al'adun Fulani.

Labarai masu alaka