Nigeria: Gobara ta kona shaguna a kasuwar Ikom

Image caption Lokacin da wuta take ci a kasuwar Sabon Gari Kano.

Akalla shaguna 40 ne suka kone, a babbar kasuwar garin Ikom na jihar Cross River sakamakon gobara a kasuwar, ranar Talata.

Wutar dai wadda ta tashi da misalin karfe 2:00 na rana, an alkanta ta da matsalar wutar lantarki.

An ce jami'an kwana-kwana ba su iya kai dauki ba bisa korafin rashin kayan aiki.

Ko a karshen makon da ya gabata, kasuwar Sabon gari a Kano da babbar kasuwa da ke Birnin Kebbi na jihar Kebbi sun ci wuta, a inda kuma aka yi asarar dukiya mai yawa.