BH: An hallaka sojoji shida a Niger

Image caption Boko Haram ta sha kai hare-hare a yankin Diffa

Ma'aikatar cikin gidan jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa, wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe sojojin kasar shida, kuma sun jikkata wasu sojojin uku.

Wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gidan da aka karanta a gidan rediyon gwamnati ranar Laraba ta ce, 'yan Boko Haram din sun yi wa sojojin kwanton bauna ne yayin da suke sintiri a kusa da garin Diffa.

Wurin da lamarin ya auku yana da nisan kilomita 20 da iyakar Nijar da Nigeria.

'Yan Boko Haram sun sha kai hare-hare a yankin Diffa, inda a baya suka kashe mutane da dama.

Yankin na Diffa yana kusa da iyakar Nigeria da Nijar.

Ga rahoton Baro Arzika:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti