Rwanda: Ana tuhumar malamai da ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rwanda na tsoron shigar kungiyar IS zuwa kasar.

Wasu malaman addinin musulunci guda 17 za su gurfana a gaban wata kotu da ke Kigali,babban birnin Rwanda, bisa zargin hannu a ta'addanci.

An dai kama malaman ne a farkon wannan shekarar saboda zargin alaka da kungiyar IS.

A watan Fabrairu ne aka harbe wani malami mai suna Imam Mouhamad Mugemangango, a lokacin da yake kokarin gujewa 'yan sanda.

'Yan sanda sun ce shehun malamin ne dallalin kungiyar IS wajen shigar da matsa cikin kungiyar.