Tanzania: Za a rage albashin manyan ma'aikata

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tun bayan hawansa mulki shugaba Magafuli yake ta kokarin kawo gyara a kasar
Shugaban kasar Tanzania John Magufuli, ya ci alwashin zabtare albashin manyan ma'aikatan gwamnati.

Ya fadawa magoya bayansa cewa ba za a yadda a ce ana biyan wasu jami'ai dala dubu 18 a wata yayin da ake biyan kananan ma'aikata dala 140 ba kacal.

Mista Magafuli ya ce zai kayyade albashin manyan ma'aikatan zuwa kimanin dala 7,000 a wata.

Shugaba Magafuli ya yi alkawarin cewa zai rage barnar da ake yi a gwamnati, a lokacin mulkinsa.

Karin bayani