Za a jibge karin dakaru a gabashin Turai

Image caption Amurka za ta kai rundunonin soji uku gabashin Turai
Rundunar sojin Amurka za ta jibge karin sojoji a arewacin Turai.

Janar Philip Breedlove - kwamandan sajin Amurka a Turai - ya ce matakin wani martani ne na takalar da Rasha ke yi a yankin.

Daga farkon shekara mai zuwa za'a tura cikakkun rundunonin soji uku tare da kayan yaki.

Wannan dai shi ne babban karin da Amurka ta yi a kungiyar ta NATO tun da aka sake samun zaman dar-dar da Moscow tun bayan yakinta da Ukraine.

Birtaniya ta zargi Rasha da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita makamai a Ukraine.

Karin bayani