Nigeria: Za a hana mata haihuwa a coci

Hakkin mallakar hoto unknown
Image caption A jihar Cross River ta Najeriya mata na son haihuwa a coci
Masu fafutuka a Nigeria na kokarin ganin an hana mata haihuwa a coci-coci.

Wannan lamari abu ne da ya zama ruwan dare a jihar Crocc River da ke kudancin kasar.

Mata da dama sun yi amanna cewa an fi samun kariya sosai idan aka haihu a coci maimakon asibiti.

Wata daga cikin irin wadannan mata ta shaida wa BBC cewa, za a iya yi mata allura a asibiti amma ba wanda zai mata addu'a.

A wasu lokutan coci-coci a Najeriya na daukar ungozomomin gargajiya aiki, wadanda ba su sami wani isasshen horo ba, kuma babu isassun kayan aiki.

Masu fafutukar sun ce da mata da dama da suka haihuwa a coci asibiti suka je da basu mutu ba sanadin haihuwar.

Majalisar dokokin kasar na duba yiwuwar samar da kudurin doka da za ta hana haihuwa a coci.