Shin ko yaya yanayin tsaro yake a filayen jirgin saman Afrika?

A ci gaba da jerin rahotanni da ake yi kan wasiku daga Afrika, mai hada fina-finai da kuma rubuce-rubuce a jarida, Farai Sevenzo, ya duba yanayin tsaro a filiaye jirgin sama a nahiyar Afrika.

Muna cikin lokaci ne na zullumi: Surfuri tsakanin birane na zuwa da fargaba iri-iri, inda mutum ke cike da tunani ko za a kai wani hari.

Mutanen Afrika na cike da damuwa irin na wannan lokaci a kasashen su da kuma kasashen turawa- ko yaya biranen Brussels da Paris zasu ji da rashin 'yan Afrikan nasu?

An yi lissafin wasu kananan masaukin otal-otal da ke kasashen Burkina Faso da bakin teku a Ivory Coast, na cikin wuraren da kungiyoyin ta'adda ke neman kai hari, ganin cewar a baya mallakin Faransa, kasar da a yanzu 'yan ta'adda suma suka sanya wa idanu.

Ba kasashen da ke harshen Faransanci ne kadai ke fuskantar barazanar ta'addanci ba, ya shafi jami'u da motocin hayanda mashayu da kasuwanni da coci-coci da masallatai a yammaci da gabashin Afrika.

Lamarin kan shafi duk al'umma, koma wacce addini ne suka dosa.

Image caption An saki duka fasinjan da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin ranar Talata.

Ana iya sace jirgi sukutum, duk kuwa da irin tsaron da ke akwai, yadda ko dan ta'adda daya tilo ko masaoyi ke iya sace jirgi- kamar irin lamarin da ya afku ga jirgin Misra, watau Egypt Air, inda mutum guda ya juya akalar jirgin zuwa Cyprus.

An san da cewa, wasu jirage kuma na dauke da makaman kare dangi.

An yi sabbin filayen saukan jirage a kasashen Afrika a kwana-kwanan nan, inda suke fatan farashin sufurin ya ragu saboda a samu saukin tafiye-tafiye tsakanin kasashe da nahiyoyi ma.

Yaki da karbar cin hanci da rashawa
Image caption "Wani jami'in tsaron sai ya amshe fasfo din ka, ya yi gabansa, yadda dole ka bashi dan wani cin hancika sake ganin kayan ka".

Tashin hankalin da ya afku a Brussels ya sa alamun tambayoyi da dama kan tsaron tashohin ruwan Afrika, musamman na Najeriya da Kenya, inda mayakan addinin Islama suka fi kamari.

Wata jaridar kasar Najeriya, ta This Day ta bayar da rahoton yadda matafiya ke cewa hotunan mayakan Boko Haram da aka wallafa basu da amfani a tashoshin sufuri, inda ta ce matsalar da ya kamata a duba, ita ce na cin hanci da rashawa tsakanin jami'an tsaro da ke aiki wajen.

Maganar dai daya ce, matafiyin da kullum ke bisa hanyar tafiya cikin hanzari, inda suke mika duk canjin da ke aljihun su ga jami'an tsaron filayen sufuri, su kuma su tabbatar da shigar kayansa cikin jirgi ba tareda matsala ba.

Akwai karnukan da ke shinshina kaya dai, duk da cewar suma muggan kwayoyi suke bincikawa ba makamai ba, don haka abun a duba shi ne wane fasinja ne ke dauke da makami.

Masani kan harkokin tsaro a filayen jiragen sama Adebayo Babatunde ya shaidawa jaridar This Day cewa, batun da ke barazana matuka ga tsaro da ayyukan sirri a filayen jiragen sama na kasashen duniya.

"Dole ne mu bi dokokin kasa da kasa, sau da kafa" In ji Adebayo.

Image caption Kungiyar mayakan Al-Shabab ta SomaliyaSomalia's al-Shabab sun dauki alhakin wani hari da aka kai cikin wani jirgi a watan da ya gabata.

Ya kara da cewa, "Idan ba duba abin da ke cikin jaka ba, to a cire ta a lalata ta, kuma gwamnatocin kasashen su hanzarta wajen samo na'urar da ke duba makamai da bama-bamai".