Chibok: 'Ba 'yarmu ce ta kai hari Kamaru ba'

Image caption A watan Afrilun 2014 ne aka sace 'yan matan Chibok daga makarantar sakandare.

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok sun ce yarinyar nan da dakarun Kamaru suka kama tana shirin kai harin kunar bakin-wake ba daya daga cikin 'ya'yansu ba ce.

Iyayen sun bayyana hakan ne bayan da suka duba hotunan yarinyar.

Shugaban iyayen 'yan matan na Chibok, Yakubu Nkike, wanda na daya daga cikin wadanda suka duba hotunan, ya ce yarinyar ba ta kama da 'yan mata na Chibok.

Ya kuma ce shekarun 'yar kunar bakin-waken bai kai 15 ba, a inda su kuma 'yan matan Chibok suke da shekaru 17 zuwa sama.

A karshen makonnan ne dai rahotanni daga kasar Kamaru suka alakanta wata mai shirin yin kunar bakin-wake da 'yan matan Chibok da aka sace.

Wannan batun dai ya janyo kace-nace a Najeriya, har ma gwamnatin kasar ta ce za ta tashi wakilai na musamman domin gano hakikanin gaskiyar al'amarin.