FBI zata kara bude wata wayar iphone

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI zata taimakawa 'yan sanda ta bude manhajar wata wayar iphone.

FBI tayi tayin wannan taimakon ne bayan ta bayyana cewa, ta samu damar bude wayar Syed Farook wanda ya aikata kisa a San Bernadino.

Kasa da kwana guda bayan bayyana bude manhajar wayar sai kuma hukumar FBI ta amince ta bude wata wayar a kokarin binciken aikata da 'yan sanda suke yi.

Syed Farook da maidakinsa an kashe su ne, bayan sun kashe wasu mutane 14 cikin watan Disambar bara.

A baya dai hukumar FBI ta bukaci kamfanin Apple ya taimaka wajen bude manhajar wayar iphone ta marigayi Syed Farook.

Amma kamfanin Apple ya ki amincewa da wannan bukata ta FBI.

Kamfanin Apple yace, bai kamata ya bada damar leka asirin masu amfani da wayoyinsa ba.