GSK ya yarda a kwaikwayi maganinsa a Afirka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption GSK ya yarda a kwaikwayi magungunansa a AFrika
Kamfanin magani na Glaxo Smith Kleine wanda aka fi sani da GSK ya amince sauran kamfanonin magani na kasashe marasa karfi kamar Afirka, su kwaikwayi magungunansu.

Kamfanin ya ce ba zai yi amfani da kalmar hakkin mallaka a kan magungunan ba domin kananan kamfanonin Afirka su samu damar yin magunguna masu saukin farashi.

Sai dai kuma GSK din ya ce zai bai wa wasu kamfanonin magani lasisi a kasashe masu matsakaicin arziki, a inda kuma za su rinka biyan kamfanin wasu 'yan kudade.

Sakamakon gasa tsakanin kamfanoni masu kwafar magunguna ne ya sanya farashin magungunan cutar HIV suka fadi.