Ana binciken Shell a Italy kan mai a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Kamfanin Royal Dutch Shell na gaba-gaba wajen haka da fitare da mai daga Najeriya.

Masu gabatar da kara na Italiya suna binciken kamfanin mai na Shell da kamfanin mai na Eni na kasar ta Italiya, a ci gaba da duba kan yadda kamfanonin suka mallaki rijiyar mai, a Najeriya.

Kamfanonin sun ce suna bayar da hadin kai wajen binciken.

Ana dai tuhumar kamfanonin ne bisa rashawa da cin hanci, a sayen rijiyar mai a Najeriya, a kan kudi $1.3bn, a 2011.

Sai dai kuma kamfanin Eni yaki amincewa da zargin, a inda ya ce ya biya kudi ga aljihun gwamnatin Najeriya kai tsaye.

A 2014 ne hukumomi a Italiya suka fara binciken kamfanin na Eni bisa zargin rashawa a harkar mai, a Najeriya.