Niger: An kama matasa kan kafar sada zumunta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Niger, an cafke wasu matasa masu dama na bangaren adawa bisa zargin yin amfani da kafafen sada zumunta domin tayar da tarzoma.

Da farko dai an kama matasan masu yawa aka kuma sanya su a kurkuku,kafin daga bisani a sake su.

Sai dai kuma har yanzu akwai mutane 10 da ke tsare, a gidan yarin.

Ana dai zargin matasan ne da yada wasu bayanai ne da ka iya haddasa fitina a cikin kasa ta hanyar shafin sada zumunta na Whatsapp.

Sai dai shugabannin matasa magoya bayan jam'iyyar ta Moden Lumana sun yi watsi da zargin suna cewa bi-tada-kullin siyasa ne.

Hamayya dai tana kara kamari tsakanin jam'iyya mai mulki ta PNDS da bangaren adawa musamman jam'iyyar Modem Lumana, tun bayan zaben shugaban kasar da Mahamadou Issoufou ya lashe.