Zan duba kasafin kudi dalla-dalla - Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yace, zai bi kasafin kudin kasar na bana da 'yan majalisa suka mika masa dalla-dalla kafin ya amince da shi.

Buhari ya kuma ce, zai duba kudin da aka warewa kowacce ma'aikata kafin ya sanya a hannu akan kasafin kudin da 'yan majalisar dokoki suka zartar cikin makn jiya.

Wasu dai na ganin wannan wata alama ce cewa, za a iya kara fuskantar jinkiri kafin soma aiwatar da kasafin kudin.

Kasafin kudin na bana dai ya fuskanci matsaloli da suka hada da wata badakalar alkaluman irin kudaden da aka warewa wasu ma'aikatu.

Shugaba Buhari yace, kafin ya sanya hannu akan kasafin kudin sai ya tabbatar da cewa, yayi daidai da abinda ya mikawa majalisar dokoki.

Kasafin kudin da aka mikawa shugaban kasar dai a dunkule yake ba tare da bayanai a fayyace ba akan kudaden da aka warewa sassan gwamnati.

Wannan dai shi ne kasafin kudin gwamnatin Shugaba Buhari na farko.