NNPC ya sasanta rikicin IPMAN

Hakkin mallakar hoto Getty

A Najeriya, a wani yunkuri na kawo karshen matsalar man fetur da kasar ke fama da ita, Shugaban kamfanin mai na kasar NNPC, kuma karamin Minista na ma'aikatar man fetur Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu, ya shiga tsakani don sulhunta takaddamar da ke tsakankanin kungiyar dillalan man masu zaman kan su, watau IPMAN, wanda ke tasiri wajen ta'azzara karancin man.

A kokarin sa na shiga tsakani, Ministan ya gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki a kungiyar ta IPMAN, zuwa ofishinsa da ke ginin NNPC Towers a Abuja babban birnin kasar, inda ya kafa kwamitin mutane 14 da zasu duba hanyoyin shawo kan rikicin da ke tsakanin masu dakon man.

Wata sanarwa daga ma'aikatar man fetur ta kasar, ta ce ministan ya yi la'akari da muhimmanci da kungiyar ta IPMAN ke da shi wajen kawo karshen matsalar karancin man fetur din da kasar ta shiga.

Dr. Kachikwu ya kuma yi kira da kungiya ta IPMAN, da ta yi aiki kafada-kafada da hukumomin gwamnati da ke ruwa da tsaki su ma wajen sa ido ga lamarin samar da man fetur a kasar, watau NNPC da DPR, domin tabbatar da cewa an samu mafita mai dorewa.

Minsitan ya sha alwashi kamar yadda ya shaidawa Majalisar Dattijan kasar cewa zai tabbatar da an kawo karshen matsalar karancin man nan da makwanni biyu masu zuwa.

A nasa bangaren, babban sakataren kungiyar dillalan man fetur din masu zaman kansu, Alhaji Danladi Pasali, ya bayyana aniyarsu ta tabbatar da samun maslaha domin ci gaban kasa, da saukaka wahalar da al'umman Najeriya suka shiga".

A wani bangaren kuma, kamfanin mai na NNPCin ya ce ya bude fage ga masu zuba jari domin kafa sababbin matatun man fetur a cikin harabar matatun man kasar da ake da su a yanzu.

Kamfanin na NNPC ya ce, kafa sababbin matatun man, zai taimaka wajen kawo karshen karancin mai a kasar, ta hanyar kara yawan man da ake tacewa a kasar a yanzu, daga gangar mai 450,000 a kowacce rana, zuwa gangar mai 650,000.