Trump ya sauya ra'ayi kan zubar da ciki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kalaman Donald Trump dai sun kasance masu haddasa kace-nace.

Daya daga cikin 'yan takarar neman shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya sauya matsayinsa na hukunta matan da suka zubar da ciki.

A wata sanarwa da ya fitar kuma ya ce, matsayinsa shi ne, likitan da ya zubar da cikin ne za a hukunta ba macen da aka zubarwa ba.

Shi dai mista Trump ya fadi cewa, idan dai aka dawo da dokar haramta zubar da cikin, to za a hukunta wadanda aka samu da laifin yi, a wata hira da ya yi da gidan talbijin na MSNBC.

'Yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar adawa ta Democratic, Hillary Clinton, ta soki Donald Trump cewa haramta zubar da ciki, dai-dai yake da ayyana mata da likitoci, a matsayin masu manyan laifuka.