Kotun MDD ta wanke Vojislav Seselj

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Vojislav Seseji yana fama da cutar daji

Kotun musamman ta Majalisar Dinkin Duniya, ta wanke dan siyasar nan na Serbia,Vojislav Seselj, wanda ake tuhuma da hannu a kan kisan gillar musulmai, a tsohuwar kasar Yugoslavia.

Mista Seselj yana fuskantar tuhume-tuhume guda tara na laifukan yaki amma alkalin kotun ya ce bai gamsu da yadda masu gabatar da kara suka kasa tabbatar da laifukan da wanda ake tuhumar ya aikata.

Ana dai tuhumar Vojislav Seselj da laifin tilastawa musulmai da 'yan kabilar Kirota barin gidajensu da cin zarafi da kuma fyade, a shekarar 1990.

Sai dai kuma mista Seselj bai halarci kotun ba wadda ke zama a Hague.

Tun dai a 2014 ne mista Seselj ya je Belgrade domin neman maganin cutar daji da ke damun sa.