Amurka za ta mayar wa Nigeria kuɗaɗenta

Hakkin mallakar hoto Buhari Campaign
Image caption Buhari ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya sha alwashin taimakawa Najeriya wajen dawo da kuɗaɗen da 'yan kasar suka sata, suka kuma ajiye su a bankunan Amurka.

John Kerry ya faɗi hakan ne yayin wata ganawa da suka yi da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a Washington.

A wata sanarwa da ofishin shugaban na Najeriya, ya fitar, shugaba Buhari ne ya mika kokensa ga Amurka da ta taimaka masa wajen yaki da rashawa da cin hanci da suka yi wa Najeriya katutu.

John Kerry ya ce Amurka za ta gana da hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya domin sanin yadda za su ɓullowa al'amarin.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari dai yana Amurka domin halartar taron kasashen duniya kan makamashin nukiliya.