Kamfanin Apple ya cika shekaru 40

Katafaren kamfanin fasaha da yayi fice a duniya wato Apple ya cika shekaru arba'in da kafawa.

Mutane uku ne suka kafa kamfanin ranar 1 ga watan Aprilun 1976 a Amurka.

Wanda yafi yin fice daga cikin wadanda suka kafa kamfanin shi ne marigayi Steve Jobs, wanda ake ganin shi ya kai kamfanin ga daukakar da yake da ita yau.

Steve Jobs ya rasu ne ranar 5 ga watan Oktoban shekara ta 2011.

Kamfanin na Apple dai yana cikin kamfanonin da suka fi karfin arziki a duniya.

Apple dai yafi yin fice ne ta fuskar yin na'urorin komfuta.

Amma daga shekara ta 2007 kamfanin ya soma kera wayar salula samfurin iphone. Kuma ya zuwa yanzu wayar iphone tana cikin wayoyin dake kan gaba a duniya.