Kamaru ta hana yin wata zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP

A Kamaru jami'an tsaro sun tarwatsa taron masu shirin gudanar da zanga zangar juyayin mutuwar mutane 12,000 da suka hallaka sanadiyar hare-haren kungiyar Boko Haram a cikin fadin kasar.

Jami'an tsaron sun dauki matakin ne na tarwatsa taron bisa umurnin Ministan tsaro.

Ministan ya bada hujjar cewa, gwamnati ta hana gudanar da zanga zanfa ne domin kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.

Kamaru dai na daya daga cikin kasashen yankin tafkin Chadi da rikicin 'yan kungiyar ta Boko Haram ya shafa.

Rikicin Boko Haram dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da haddasa hasarar dimbin dokiyoyi.