Ghana: Wuta ta tashi a gidan rawa

Hakkin mallakar hoto STEVEN ANTI
Image caption Kasashen Afirka na fusknatar barazana daga tashin gobara

Wuta ta tashi a wani katafaren gidan shaƙatawa da ke birnin Accra na Ghana.

Gidan dai ya ƙUnshi mashayar giya da dakin cin abinci da wurin caca da kuma dakin rawa.

Wakilin BBC ya ce wutar ta lashe ginin gabaɗayansa sakamakon shafe sa'a biyu da ta yi tana ci, ba tare da jami'an kwana-kwana sun kai dauki ba.

An ce dai ko da jami'an na kwana-kwana suka je wurin, ba su iya kashe wutar ba saboda ruwan da suke da shi ya kare.