Cutar Lassa ta bulla a Jamus

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Bera ke jawo cutar zazzabin Lassa
An samu bullar cutar zazzabin Lassa a Jamus, karo na farko da cutar ta bulla a wata kasa da ba Afrika ba.

Wani ma'aikaci a wajen kintsa gawa ne ya kamu da cutar bayan ya yi mu'amala da wani Ba'amurke da cutar ta hallaka a watan Fabrairun 2016.

Ba'amurken wani babban Likita ne a asibitin mishinary da ke Togo, inda aka mayar da shi Jamus bayan ya kamu da cutar, ya kuma mutu a can.

Hukumar lafiya ta duniya da asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya da cibiyar da ke yaki cututtuka masu yaduwa da sauran kungiyoyin agaji, suna taimakawa hukumomin kasashen da aka samu bullar cutar don daukar matakin gaggawa na shawo kanta.

Cutar zazzabin Lassa ta hallaka fiye da mutane 160 a Afrika ta Yamma, mafi yawansu daga Najeriya tun watan Nuwambar 2015.