Liberia: Ebola ta kashe wata mata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola ta hallaka dubban mutane a yankin yammacin Afrika

Jami'an kiwon lafiya a Liberia sun ce wata mata ta mutu sakamakon cutar Ebola, watanni bayan an bayyana kawo karshen cutar a kasar.

Matar mai shekaru 30 ta mutu ne a Asibitin Redemption, da ke garin New Kru mai cunkoson jama'a a Monrovia babban birnin kasar.

A watan Janairu ne aka bayyana cewa babu sauran cutar Ebola a Liberia, amma an samu cutar a 'yan wasu wurare a yankin.

A 'yan makwanin da suka wuce an samu mutane da dama da ke dauke da cutar a kasar Guinea mai makwabtaka.

Sama da mutane dubu 11 da 300 ne suka mutu sakamakon cutar ta Ebola cikin shekaru biyun da suka wuce, yawanci dukkansu a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.